Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Ta Tabbatar Da Kakkabo Wani Jirgin Yakinta A Siriya


Wasu jiragen Rasha a Siriya
Wasu jiragen Rasha a Siriya

Ma’aikatar Tsaron Rasha ta ce jiya Asabar an kakkabo daya daga cikin jiragen yakinta a daura da garin Saraqeb da ke karkashin ikon ‘yan tawayen Siriya, kuma ‘yan tawayen sun hallaka matukin jirgin bayan da ya diro kasa da taimakon laima

Ma’aikatar Tsaron Rasha ta ce jiya Asabar an kakkabo daya daga cikin jiragen yakinta a daura da garin Saraqeb da ke karkashin ikon ‘yan tawayen Siriya, kuma ‘yan tawayen sun hallaka matukin jirgin bayan da ya diro kasa da taimakon laima.

Kungiyar saka ido a Siriya da kuma kungiyar kare hakkin dana dam a Siriyar mai hadikwata a Burtaniya sun tabbatar da faruwar al’amarin, tare da bayanin cewa keftin din na tuka jirgin Rasha mai inji biyu, samfurin Su-25 jet mai tafiya kusa da kasa wanda aka kirkiro saboda da taimaka ma sojojin da ke kasa. To saidai shaidu sun ce an kashe keftin din jirgin ne bayan da ya bude wuta kan ‘yan tawayen da su ka yi yinkurin kama shi.

Kafar labarai ta Reuters ta ce kungiyar nan ta Tahrir al-Sham mai ra’ayin jihadi, wadda ke da alaka da tsohuwar kungiyar nan ta al-Kaida shiyyar Siriya, ta yi ikirarin kakkabo jirgin da makami mai linzamin da ake sabawa a kafada.

Rahotanni na nuna cewa wannan ne karon farko da ‘yan tawayen Siriya su ka harbo wani jirgin yakin Rasha tun daga kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG