Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ISIS Ta Rungumi Kaddara; Ta Sallamar Da Raqqa?


Shugaban ISIS Abu Bakr al-Baghdadi

A wani al'amari na tarihi kuma mai kama da rungumar kaddara, kungiyar ISIS, kamar yadda dai aka ruwaito, ta bukaci a bar mayakanta su fice daga hedikwatarsu ta Raqqa salun-alun cikin dare. Ma'ana sun sallamar da hedikwatar.

Wani mai magana da yawun kungiyoyin mayakan Siriya, ya fadi ranar Asabar cewa da yiwuwar mayakan ISIS su fice daga Raqqa a karkashin wata yarjajjeniyar da aka cimma tsakaninsu da mayakan Siriya da ke samun goyon bayan Amurka da su ka masu zobe.

Mai maganar ya ce da yiwuwar mayakan na ISIS su fice daga birnin cikin dare, daga jiya Asabar zuwa yau Lahadi. Duk wani dan bindigar ISIS da ya tsaya, za a tilasta shi au ya mika wuya au a kashe shi.

Tun daga ranar Jumma’a farar hula su ka fara tserewa daga Raqqa, gabanin dannawa ta karshe da ake sauraron mayakan da ke samun goyon bayan Amurka za su yi, da zummar sake kwace birnin daga ISIS.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG