Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Fara Gwajin Allurar Rigakafin COVID-19 Kashi Na Hudu


Lokacin da ake yi wa wata mata rigakafin COVID-19
Lokacin da ake yi wa wata mata rigakafin COVID-19

Likitoci a Isra'ila sun fara ba da kashi na hudu na rigakafin mai kara kuzari na COVID-19 a ranar Litinin a zaman wani bangare na binciken gwaji don tantance ko karin harbin na iya bunkasa karfin rigakafi daga cutar.

Nazarin gwajin da ya shafi ma'aikata kusan 150 a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Sheba da ke kusa da Tel Aviv na zuwa ne kwanaki kadan bayan wani kwamitin ba da shawara kan kiwon lafiya ya ba da shawarar.

Kwamitin ya ba da shwarar cewa mutanen da suka haura shekaru 60 da haihuwa, da wadanda ba su da karfin gina jiki da kansu da ma'aikatan kiwon lafiya, sun karbi kashi na hudu na allurar rigakafin Pfizer.

Isra'ila ta zarce yawancin duniya wajen yiwa 'yan kasarta rigakafin, gami da bayar da allurar rigakafin na uku wato booster,.

Amma matakin ya ragu a cikin 'yan makonnin nan yayin da take fuskantar bullar sabbin nau’in COVID-19 na biyar da omicron na coronavirus ya haifar.

Abun da yayi sandiyar rufewar filayen jiragen sama a duniya tun lokacin da aka fara gano shi a watan da ya gabata a wasu kasashe.

XS
SM
MD
LG