Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Kai Hari A Zirin Gaza


Bayan da Isra'ila take zargin kungiyar Hamas da kai wani hari na roko zuwa kudancin kasarta, yanzu haka sojojin kasar sun kai wasu hare hare a gine gine mayakan Hamas daban bdaban a yankin Zirin Gaza.

Jiragen yaki na sojan sama na Isra’ila sun yi luguden wuta akan sansanonin Hamas daban-daban a Zirin Gaza a yau juma’a.

A wani martini da Isra’ila ta maida akan harin rokokin da aka cilla a kudancin kasarta, har suka lalata wata makarantar Yahudawa.

Rundunar sojan sama ta Isra’ila ta fada a cikin wata sanarwa cewa, jiragen yakin wasu gine ginen mayakan Hamas dake warwatse a duk fadin yankin Zirin Gaza suka auna.

Sai dai har yanzu duka bangarorin biyu babu wanda ya bada sanarwar rasa rayuka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG