Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Da Falasdinawa Sun Fara Musanyar Fursunoni


Bafalasdine yana buga Posta na Falasdinawa a zirin gaza, yayin da ake shirin musanyar fursunoni da Isra'ila
Bafalasdine yana buga Posta na Falasdinawa a zirin gaza, yayin da ake shirin musanyar fursunoni da Isra'ila

Yau talata Isra'ila ta ke sako ayarin farko na Falasdinawa fursunoni 477, yayin da kungiyar Hamas zata sako sojan Isra'ila Gilad Shalit.

Isra’ila da kungiyar Hamas sun fara gudanar da shirinsu na musanyar fursunoni inda za a musanya daruruwan Falasdinawa dake kurkukun Isra’ila da wani sojan Isra’ila mai suna Gilad Shalit da aka kama.

Kwambar motoci dauke da Falasdinawan da za a sako yau talata sun taso daga gidajen kurkuku na Isra’ila zuwa tasoshin bakin iyaka kafin asubahin yau talata.

Yarjejeniyar musanyar ta tanadi sako Falasdinawa fursunoni su 477 a yau talata, yayin da za a sako karin 550 a cikin watanni biyun da ke tafe.

Ita kuma Hamas zata sako wannan sojan Isra’ila Gilad Shalit. Za a mika sojan na Isra’ila ga Masar wadda ita kuma zata mika shi ga Isra’ila a daidai lokacin da aka fara sako Falasdinawan.

A bayan sako shi, za a dauki Shalit zuwa wani sansanin mayakan sama inda firayim minista Benjamin Netanyahu da sauran shugabanni da kuma iyalansa zasu tarbe shi.

Daga cikin Falasdinawa 477 da za a sako yau talata, za a tasa keyar 100 zuwa yammacin kogin Jordan, za a kori kimanin 40 zuwa gudun hijira a Jordan da Turkiyya da Qatar da kuma Syria. Sauran kuma za a sake su su koma Gaza inda Hamas ta shirya musu tarba ta gwarzaye.

XS
SM
MD
LG