Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya Ta Maida Martani Kan Kurdawa 'Yan Tawayen Da Ke Iraqi


Sojojin kasar Turkiyya dauke da akwatunan gawarwakin 'yan uwan su da kungiyar PKK ta kashe a cikin harin da ta kai mu su.

Sojojin Turkiyya sun maida martani sannan suka tsallaka har cikin Iraqi suna farautar yan tawayen Kurdawan.

Kurdawa ‘yan tawaye sun kashe sojojin Turkiya ashirin da shidda suka kuma raunata goma sha shidda a kusa da kan iyakar Turkiyya da Iraqi.

Hukumomin Turkiyya sunce 'yan tawaye daga kungiyar PKK sun bude wuta akan sansanonin soja a Cukurca da Yuksekova a lardin Hakkari dake kudu maso gabashin kasar.

Rahotannin sunce sojojin Turkiyya sun maida martani sannan suka tsallaka har cikin Iraqi suna farautar yan tawayen Kurdawa. Haka kuma an bada rahoton cewa Jiragen yakin Turkiyya sun kai hare haren ramuwar gaiya.

Shugaban Turkiya Abdullahi Gul ya fadawa 'yan jarida, ramuwar gaiyar wadannan hare hare ba zasu yiwa Kurdawa kyau ba. A dai yan makonin da suka shige kungiyar PKK ta Kurdawa ta zafafafa hare hare akan Turkiyya.

Tsoffin sojojin kasar Turkiyya su na zanga-zanga a kofar ofishin Frayim Minista Tayyip Erdogan don nuna rashin yarda da harin baya-bayan nan da Kurdawa 'yan tawayen PKK su ka kaiwa sojojin kasar ta Turkiyya.
Tsoffin sojojin kasar Turkiyya su na zanga-zanga a kofar ofishin Frayim Minista Tayyip Erdogan don nuna rashin yarda da harin baya-bayan nan da Kurdawa 'yan tawayen PKK su ka kaiwa sojojin kasar ta Turkiyya.

-

XS
SM
MD
LG