Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Israila Ta Dauki Tsauraran Matakai Akan Falesdinawa


Firayim Ministan Israila Benjamin Netanyahu

Jiya Lahadi Firayim Ministan Israila Benjamin Natanyahu ya sanar cewa kasarsa ta dauki wasu tsauraran matakai akan Falasdinawa masu tsatsauran ra'ayi tare da cewa kasar "tana yakin mutuwa da 'yan ta'ada"

Jim kadan bayan ya dawo daga New York inda ya je taron Majalisar Dinkin Duniya, Netanyahu tare da wasu manyan jami'an tsaron kasar Israila suka yi wani taron gaggawa dangane da yawan tashin hankali da Falasdinawa ke haddasawa kan Israilawa.

Firayim Ministan ya ce zasu hanzarta rushe gidajen 'yan ta'ada. Zasu kara yawan jami'an tsaro a birnin Qudus tare da West Bank. Bugu da kari Israila zata daure duk wanda ake kauatata zaton dan ta'ada ne ba tare da bata lokaci ana wata doguwar shari'a ba.

Tun farko 'yansandan Israila suka sanarda dakatar da Falasdinawa daga shiga tsohon birnin Qudus. Ban da haka duk namiji mai shekaru kasa da 50 ba za'a bari ya shiga Masallacin al-Aqsa ba.

Masallacin na cikin daya daga wurare masu tsarki ga addinin musulunci kuma nan ne aka fi samun tashin hankali cikin 'yan kwanakin nan.

Wasu Israilawan da Falasdinawa masu sassaucin ra'ayi sun damu da yawan tashin hankali abun da suka ce wata alama ce dake nuni da barkewar tashin hankalin gama gari nan gaba.

XS
SM
MD
LG