Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Israila Ta Haramtawa 'Yan Kasar Indonesia Shiga Kasarta


Firayim Ministan Israila, Benjamin Netanyahu

Israila ta haramtawa 'yan yawon bude ido da masu ibada daga kasar Indonesia shiga kasarta saboda kwana kwanan nan 'yan Indonesia suka yi zanga zanga a harabar ofishin jakadancin Amurka tare da kona tutocin Amurka da Israila akan bude ofishin jakadancin Amurka a Birnin Qudus

Kasar Ira’ila ta haramtawa yan yawon bude ido da masu ibada daga kasar Indonesia shiga kasar ta. Ta dauki wannan mataki ne domin maida martini ga mataki makamancin wannan da ta ce Indonesia ta dauka akan yan Isira’ila.

Duk shekara dubban yan kasar Indonesia Musulmi kan kai ziyara kasar Isira’ila a zaman wani bangare na ziyarar da suke yi a gabas ta tsakiya..

To amma yan Indonesia sun nuna rashin amincewarsu akan musgunawa Palasdinawa da suka cewa Isira’ila tana yi. Domin a farkon wannan wata masu zanga zanga yan kasar ta Indonesia suka kona tutar Amurka dana Isira’ila a harabar ofishin jakadancin Amurka dake birnin Jakarta domin nuna rashin amincewar su da maida ofishin jakadancin Amurka zuwa birnin Kudus daga birnin Tel Aviv.

Wannan alamari yana faruwa ne a yayinda alamu ke nuna dangantaka tsakanin kasashen biyu tana ingantuwa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG