Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Isra'ila Ta Kai Hari A Gaza Lahadin Nan.


'Yansanda suke tsaye kan gawar wani Ba-Falasdine.

Wata mace mai juna biyu da 'yarta sun halaka sakamakon farmakin.

Isra'ila ta kaddamar da hari da jiragen yaki a safiyar lahadin nan a zirin Gaza, ta kashe wata mace mai juna biyu da wata 'yarta karama.

Rundunar Sojin Isra'ila ta ce ta kai harin ne a zaman martani kan wani hari da roka da aka kaiwa kasar daga yankin da Hamas take iko. Rundunar ta fada jiya Asabar cewa garkuwa daga makamai masu linzami ta cafke wani roka a garin Hof Ashkelon, dake arewacin Gaza.

Masu aikin kiwon lafiya a Gaza suka ce matar da 'yarta sun mutu ne lokacinda ginin gida da suke ciki rushe sakamkon harin. Wasu mutane masu yawa kuma sun sami raunuka.

Haka nan a yau lahadi, rundunar sojin Isra'ilar tace wata ba Falasdiniya ta tada bam da aka boye cikin wata mota a wani wurin duba motoci a yammacin kogin Jordan, ta raunata dansanda daya.

Wannan harin ya kuma biyo bayan karin hare hare da wukake a bangaren tsohon birnin kudus a jiya Asabar.

A harin farko wani dan shekaru 16 ya dabawa yahudawa biyu wuka kamin a harbe shi har lahira.

Daga bisani wani dan shekaru 19 da haifuwa ya dabawa 'Yansanda biyu, kamin shima 'Yansanda suka harbe suka kashe shi har lahira.

Jerin hare haren duk suna aukuwa ne a gabshin birnin kudus a kewayen masallacin al-Aqsa, da yake da matukar daraja ga musulmi, da yahudawa wadanda suke kiransa Temple Mount.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG