Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ja’afar Ja’afar Ya Bayyana A Gaban Kwamitin Majalisar Dokokin Kano


A lokacin da Ja'afar Ja'afar (Hagu) ya isa Majalisar Dokokin Jihar Kano domin ba da bahasi kan zargin rashawa, dauke da Al Qurani mai Girma
A lokacin da Ja'afar Ja'afar (Hagu) ya isa Majalisar Dokokin Jihar Kano domin ba da bahasi kan zargin rashawa, dauke da Al Qurani mai Girma

Gayyatar ta Ja’afar ta haifar da ra’ayoyi mabanbanta a tsakanin al'umar ciki da wajen Kano, musamman ma a shafukan sada zumunta kan tsaron lafiyarsa, inda yayin da wasu ke cewa kada ya je wasu kuwa suka nuna ya kamata ya akasin hakan.

Mawallafin jaridar yanar gizo ta Daily Nigerian, Ja’afar Ja’afar, wanda ya wallafa wasu hotunan bidiyo da suke zargin gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje yana karbar rashawar miliyoyin daloli, ya bayyana a zauren majalisar dokokin jihar domin ba da bahasi kan sahihancin bidiyon.

Kwamitin ya saurari bahasin ne karkashin jagorancin Hon. Baffa Babba Dan Agundi, wanda ya fara da tambayar Ja’afar inda ya samu bidiyon.

“Za ka iya fadawa wannan kwamitin waye ya ba ka wadannan bidiyo, tun da ka ce ba kai ne ka yi su ba?” Inji Dan Agundi.

Sai Ja’afar ya ce “ka’idar aiki ta ce a sakaya sunan shi, inda ka’idar aiki ta ce a fade shi zan fada.”

Mawallafin jaridar yanar gizon ta Daily Nigerian ya kara da cewa, “kafin mu buga wadannan faifan bidiyo sai da muka tabbatar da sahihancinsu domin saboda girman abin sai an yi taka tsantsan.”

Kusan makwanni biyu da suka gabata, Ja’afar ya wallafa hotunan bidiyon wadanda suka nuna gwamna Ganduje yana zuba kunshin daloli a aljihun rigarsa.

Hotunan bidiyon sun haifar da ce-ce-ku-ce a ciki da wajen jihar ta Kano, inda har ya yi zargin cewa ana yi wa rayuwarsa barazana.

A makon da ya gabata Majalisar Dokokin jihar ta Kano ta kafa kwamitin bincike inda aka fara zaman a yau.

Gayyatar ta Ja’afar ta haifar da ra’ayoyi mabanbanta a tsakanin al'umar ciki da wajen jihar ta Kano, musamman ma a shafukan sada zumunta, inda yayin da wasu ke cewa kada ya amsa gayyatar gudun barazana ga lafiyarsa wasu kuwa cewa suka yi ya amsa kiran.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari kan wannan zaman jin bahasi:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG