Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattijan Najeriya ta amince da dokar zabe


Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Da Shugaban Majalisar Dattijai Abubakar Bukola Sarki
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari Da Shugaban Majalisar Dattijai Abubakar Bukola Sarki

Majalisar Dattawan Najeriya ta amince da dokar zabe karo na hudu, bayan ta yi mata garambawul. Wannan doka ita ce wace Hukumar Zabe za ta yi amfani da ita a zaben shekara ta 2019.

Wanan dokar zabe da majalisar dattawa ta amince da ita tana kunshe ne da muhimman batutuwa da hukumar zabe za ta yi amfani da su a zabe mai zuwa.

Abubuwan da suka fi daukan hankali guda biyar ne, akwai batun na'urar tantance masu kada kuri'a ,da ranar kammala zaben fid da gwani, da tanadi game da cire alamar jam’iya ko dan takara, adadin kudin da za a kashe a yakin neman zabe da kuma hukuncin dauri idan an samu mutum da katin zabe na jabu ko kuma na wani daban ba nashi ba.

Bisa ga bayanin da aka yiwa Sashen Hausa a kan wannan doka, idan ba a kawo kad rida ba har tsawon sa'o'i uku kafin a fara zabe, to sai a daga wanen zaben sai washe gari. Duk gyaran da ya kamata a yi a dokar an yi har da maganan zaben fid da gwani. Dole ne a kamalla su kwanaki 90 kafin zabe. Akwai maganar alamar jam’iya da kuma duk wanda aka kama da katin zabe na jabu za a daure shi shekaru biyar a gidan kaso,wanda kuma ya zo da katin wani za a daure shi shekara biyu. An kuma soke maganar rajistar masu kada kuri'a a dokar. Idan babu kad riba babu zabe.

Majalisar dattawan ta yi fatan shugaba mohammadu Buhari zai ratabba hannu a dokar ganin cewa sau uku yana mayar wa majalisar da ita ba tare da ya sa hannu ba, dai dai ‘yan majalisan sun ce gyare gyaren da aka yi zai kara inganta demokradiyar kasar.

Saurari cikakken rahoton Madina Dauda

Majalisar Dattijai ta amince da dokar zabe-4:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:05 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG