Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Taimaki Najeriya Kan Zaman Lafiya Inji Jakadanta


Jakadan Amurka a Najeriya da Gwamnan Taraba
Jakadan Amurka a Najeriya da Gwamnan Taraba

Yayin da ake kokarin gano bakin zaren magance tashe-tashen hankulan da ke da nasaba da rikicin makiyaya da manoma a wasu jihohin Najeriya, gwamnatin kasar Amurka ta sha alwashin taimakawa wajen magance irin wadannan matsaloli.

Jakadan Amurka a Najeriya William Stuart ya bada tabbacin taimakawa Najeriya wajen samun zaman lafiya, ya fadi haka ne yayin wata ziyarar da ya kai jihar Taraba, daya daga cikin jihohin da ke fama da irin wadannan tashe-tashen hankula na makiyaya da manoma. William yace Najeriya kasa ce dake da albarkar ma’adanai da wuraren noma da kiwo ga yawan jama’a.

To sai dai kuma abin takaici ne yadda tashe-tashen hankula a kasar kan mayar da hannun agogo baya. Ya kuma ce ya zo jihar ne don ya ga yadda take da kuma al’ummunta. Ya kara da cewa 'yan Najeriya su sani ba zasu kasance 'yan Najeriya ba muddin babu kasar Najeriya. Don haka yayi kiran da a kai zuciya nesa. A karshe ya tabbatar wa jama'a cewa kasarsa ta Amurka a shirye take wajen taimakawa da dabarun magance irin wadannan tashe-tashen hankulan da ke faruwa, musamman ma a wasu jihohin Najeriya.

Shima a jawabinsa gwamnan jihar Taraban Arc. Darius Dickson Isiyaku, ya tabo halin da jihar ke ciki inda yayi zargin shakulatin bangaro daga gwamnatin tarayya. Gwamnan yace a kokarin da gwamnatinsa ne na samar da zaman lafiya ya kafa dokar hana kiwo, dokar dake ci gaba da jawo cece-kuce, wanda hakan tasa yace suna masu mika kokon bararsu ga kasar Amurka data tallafa musu don samu zaman lafiya a jihar da ma sauran sassan Najeriya.

Tun dai bayan kafa dokar hana kiwo da wasu jihohi suka kaddamar ciki har da Taraba, rayuka da dama ne suka salwanta.A saurari rahoton Abdulaziz Ibrahim da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG