Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jakadun Kwamitin Sulhu Sun Ziyarci Yankin Tafkin Chadi


Tafkin Chadi .
Tafkin Chadi .

Wakilan kwamitin sulhu sun tashi zuwa Afirka ta yamma domin ganewa kansu matsalolin tsaro da kasashe dake raya tafkin Chadi da kuma mummunar yanayin zamantkewa da suke fuskanata a yankin.

Jakadu daga kasashe 15 dake kwamitin sulhun mai fada a ji zasu yi tattaki zuwa Kamaru da Chadi, da Nijar, da Najeriya a ziyarar aiki da zata dauki kwanaki hudu.Wannan shine karo na farko da kwamitin sulhun zai kai irin wannan ziyara zuwa yankin tafkin Cadi.


"Muna sane da barazana ga zaman lafiya a tsakanin kasashen duniya, da kuma zaman lafiya da tsaro a wadannan kasashe hudu," shugaban kwamitin sulhu na yanzu wanda shine kuma jakadan Ingila kuma jagoran tawagar,Mathew Rycroft, ya gayawa Muryar Amurka, yana hanunka mai sanda ga rikicin Boko Haram a yankin, wand a ya haddasa mummunar yanayin zzamantakewa a yankin tun bullar kungiyar a shekara ta 2009.


Kamar yadda hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD ta fada, fiyeda mutane milyan biyu ne aka tilastawa barin muhallansu a arewa maso gabashin Najeriya tun a shekara ta 2014, kuma kusan mutane dubu 190 sun zama 'yan gudun hijira a makwabtan kasashen kamariu, da Nijar, da Chadi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG