Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Adawa Ta Yi Nasara a Zaben Magajin Garin Istanbul


Jami’iyar adawa a Trukiya tayi gagarumar nasara a zaben magajin birnin Istanbul mai tattare da matsaloli. Wannan nasara wata babbar koma baya ce ga shugaban kasar Racep Tayyip Erdogan wanda ya sha kashi a Istanbul da ake ganin yafi tasiri tsawon shekaru 25.

Mai takara a jami’iyar Erdogan Binali Yildrim ya gaggauta amincewa da rashin nasara da ya kuma taya abokin takararsa Ekrem Imamoglu murna.

Shima shugaba Erdogan ya taya Imamoglu murna a wani sakon Twitter, Erdogan yace a wannan karo ma abin da kasa ke so ya tabbata.

Sakamakon da suka fara fitowa sun nuna Imamoglu yana kara samun nasara da rata mai yawa inda ya samu kuru’u sama da dubu dari bakwai wanda ya yi daidai da kashi 54 cikin dari.

A lokacin da labarin nasarar Imamoglu ya fito, mutane a fadin birnin baki daya sun gudanar da shagululan murna tare da bushe bushe da motoci a cikin gari

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG