Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Guaido Ya Bukaci Majalisar Dinkin Duniya Ta Sauke Maduro


Shugaban 'yan adawan Venezuela-Juan Guaido
Shugaban 'yan adawan Venezuela-Juan Guaido

Shugaban ‘yan adawa a kasar Venezuela Juan Guaido a jiya Juma’a yace ya fada a yayin wata ganawa da shugabar hukumar kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya Michelle Bachelet muhimmancin kawar da shugaba Nicholas Maduro domin kawo karshen wahalar da mutane ke sha.

Bachelet ta gana da Guaido ne a birnin Caracas a ranar karshe ta ziyarar da ta kai a Venezuela, an kuma shirya zata gana da Maduro a lokaci daban kafin ta bar kasar.

Guaido ya fadawa manema labarai bayan ganawar cewa ziyarar Bachelet zata taimaka wurin samar da masalaha ga bala’in da kasar ke fama da shi kana ziyarar zata kara kaimi a fafutukar da ake yi a Venezuela.

Sai dai shugaba Maduro yana tsaye a kan bakarsa cewa kokari da Guaido ke yi ya fito ne daga goyon baya da Amurka ke bashi da zummar yin juyin mulki.

Shugabannin adawar kasarsun ce za a gudanr da zanga zangar wuni guda domin nuna yanda gwamnati ke take hakkin bil adama. A ranar Alhamis da ta gabata, masu zanga zanga sun mamaye titunan kasar domin janyo hankalin kasashen duniya a kan fursinonin siyasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG