Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar APC Na Shirin Taronta Na Tsaida Dan Takarar Shugaban Kasa


Taron jam'iyyar APC
Taron jam'iyyar APC

Sahihan bayanai na nuna cewa masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC na daukar matakan karshe don cankar wanda su ke ganin ya dace ya zama dan takararsu a babban zaben 2023, wannan na zuwa ne bayan zabar tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar a matsayin dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP.

Kalaman uban jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu da ke nuna shi ya taimaka wa shugaba Buhari ya yi nasara a zaben shekarar 2015, ya sa wasu da ke neman damar yi masa zarra ko kawar da shi daga takara cewa bai cancanci samun tikiti ba.

Dan kwamitin mara baya ga shugaba Buhari Ibrahim Musa, ya ce ya zama wajibi Tinubu ya nemi afuwar shugaba Buhari da jam'iyyar APC akan kalaman.

Shi ko marubuci a jaridar Leadership Hayatu Muhammad Hussaini, cewa ya yi fidda dan takara daga arewa don ya fafata da Atiku shi ya zai dace a jam'iyyar APC duba da cewa 'yan kudu maso yammaci da gabashin kasar basu hada kansu ba.

A nasa bangaren, Sanata Abu Ibrahim ya ce mafi adalci shi ne mulki ya koma kudu.

Tuni dai dandalin Eagle Square da ke birnin tarayya Abuja inda za a gudanar da zaben fidda gwanin jam'iyyar APC ranar Litinin ya dau harama.

Shugaban kwamitin tantance ‘yan takara na APC John Odigie Oyegun ya ce cikin ‘yan takara 23, 22 sun amince su janye don samun dan takara daya ta hanyar daidaitawa, amma daya daga ciki bai amince ba ya bukaci a gudanar da zabe sai dai in shi za a tsayar. Ana rade-radin Bola Tinubu ne wanda ya ki amincewa da matakin.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:10:30 0:00

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG