Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NASARAWA: Wasu ‘Yan Takara Sun Janye Daga Shiga Zabe Saboda Sauye-Sauyen Daliget Da Ake Zargin APC Ta Yi


Shugaban Jam'iyya APC na jahar Nassarawa, John Mamman
Shugaban Jam'iyya APC na jahar Nassarawa, John Mamman

Jami’iyyar APC a Jahar Nasarawa ta zargi uwar jami’iyyar da neman haddasa rudani da rarrabuwar kawunan ‘ya’yan jami’iyyar a Jahar, biyo bayan sauya sunayen  wassu deliget da zasu gudanar da zaben fidda gwani na ‘yan takarkaru.

A wata ganawa da manema labarai, shugaban jami’iyyar APC a Jahar Nasarawa, Mr John Mamman ya bayyana cewa wasu ‘yan Takara da dama sun janye daga shiga zaben saboda sauye-sauyen sunayen deliget da uwar jami’iyyar tayi.

Honarabul Ahmad Aliyu Wadada dake neman takarar majalisar dattawa a yammacin Jahar Nasarawa ya bayyana takaicinsa kan yadda har yanzu an kasa gudanar da zaben fidda gwanin a yankinsa.

Shima wani mazaunin garin Lafiya, Alhaji Salihu Unguwar Magaji yace masu ruwa da tsaki sun tirsasa wa deliget zaben ‘yan Takara da basu da amincewar al’umma.

Duk kokarin ji daga bakin uwar jami’iyyar APC a Abuja yaci tura, duk da aika sako da kuma kiran mamba a komitin gudanarwa na jami’iyyar APC, Dattawu Ali Kumo bai sami sukunin amsa kira ta ko maido min da amsar sakon ba.

Bayan kammala zaben fidda gwanin, gwamna mai ci a Jahar Nasarawa, Injiniya Abdullahi Sule, shine ya sami tikitin takarar gwamna a jami’iyyar APC a Jahar Nasarawa yayinda David Umbugadu ya sami tikitin takarar gwamna a jami’iyyar PDP.

Mr Nentawe Yilwatda shine ya sami tikitin tsayawa Takara a jami’iyyar APCn Jahar Filato yayinda jami’iyyar PDP a jahr ta tsaida Honarabul Caleb Mutfwang don yin takarar gwamna.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00
TASKAR VOA: Fim Da Aka Shirya Kan Leah Sharibu Ya Samu Lambar Yabo
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Kalubalen Da Masu Fama Da Lalurar Galhanga Ke Fuskanta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Tasirin Cibiyar Kula Da Lafiyar Mata Da Yara Ta HopeXchange A Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hukumomi Sun Fara Shirin Bada Gudumawar Jini A Fadin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:54 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG