Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Democrat Ta Karbe Iko a Dukkan Majalisun Amurka


Mataimakiyar shugaban kasa, Kamala Harris, lokacin da take rantsar da sabbin 'yan Majalisar Dattawa uku.

A karon farko cikin shekaru sama da goma jam'iyyar Democrat ta Amurka ta samu rinjaye a dukkan Majalisun Amurka.

'Yan Jam’iyyar Democrat sun karbe ikon Majalisar Dattawan Amurka, lokacin da mataimakiyar shugaban kasa, Kamala Harris ta rantsar da sabbin mambobi uku don baiwa jam’iyyar ‘yar tazara a Majalisun biyu da kuma fadar White House a karon farko cikin shekaru goma.

Sanata Raphael Warnock, da Jon Ossiff daga jihar Georgia, da Alex Padilla daga jihar California, sun karbi rantsuwar kama aiki, ‘yan sa’o’i bayan da aka rantsar da Biden.

Sanata Warnock da Ossoff, sun lashe zaben su ne a zagaye na biyu na zaben da aka yi a ranar biyar ga wannan watan na Janairu, zaben na su yasa Majalisar ta rabu diga biyu kowace jam’iyya na da mambobi 50.

Shi kuwa Sanata Padilla, an nada shi ne don ya maye gurbin mataimakiyar shugaban kasa Kamala, wadda ta ajiye aikin ta a ranar Litinin, aka kuma rantsar da ita jiya a matsayin mataimakiyar shugaban kasa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG