Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Labour Ta Ce Zata Kalubalanci Sakamakon Zaben Shugaban Kasa A Kotu


Yusuf Datti Baba-Ahmed
Yusuf Datti Baba-Ahmed

'Yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa a Najeriya sun ce za su kalubalanci sakamakon zaben da ya ayyana dan takarar jam'iyya mai mulki a matsayin wanda ya yi nasara.

Zaben da aka yi na ranar Asabar ya fuskanci matsalolin na’ura da na ma’aikata, lamarin da ya sa aka jinkirta kada kuri’a da kwana daya ko fiye da haka a wasu rumfunan zabe.

Jam’iyyar Labour ta gana da manema labarai da magoya baya a ranar Laraba da rana, sa’o’i bayan da hukumar zaben INEC ta ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zabe.

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Peter Obi bai halarci zaman na ranar Laraba ba amma mataimakinsa Yusuf Datti-Ahmed ya fada wa manema labarai cewa shi da Obi zasu kalubalanci sakamakon a kotu. Bayan haka Datti ya bukaci ‘yan jam’iyyar da magoya ba da su kwantar da hankalinsu.

Babbar Jam’iyyar Adawa Ta PDP Ta Samu Nasara A Kotu Na Gudanar Da Zaben Gwamna
Babbar Jam’iyyar Adawa Ta PDP Ta Samu Nasara A Kotu Na Gudanar Da Zaben Gwamna

Wani babban mai kalubalantar sakamakon zaben shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP. Jam’iyyar Labour da PDP sun yi wani taron hadin gwiwa ranar Talata inda suka kira sakamakon zaben shirme, ‘yan sa’o’i kafin hukumar INEC ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zabe.

An dai samu rahotannin rikicin siyasa da tilasta kada kuri’a da magudi a wasu wurare.

Rotimi Olawale, mai sharhi ne a kan siyasa kuma daya daga cikin shugabannin da suka kafa cibiyar Youth Hub Africa, ya ce wasu daga cikin matsalolin da suka fuskanta a ranar Asabar na kayan aiki ne, hukumar INEC ta fuskanci kalubale a wannan bangaren. Abin takaici, INEC ta yi alkawura da dama kuma ta gaza cika wa, a wurare da dama kuma jami’iyyu dabam-daban sun yi yunkurin hana yin zabe. Shi ma wannan ya kawo shakku kan tsarin zaben."

Dan takarar jam'iyyar Labour Peter Obi da mataimakinsa Datti Ahmed.
Dan takarar jam'iyyar Labour Peter Obi da mataimakinsa Datti Ahmed.

Bisa ga sakamakon zaben da aka bayyana a hukumace, Tinubu ya samu kuri’u kusan miliyan 8.8, daga nan sai Atiku Abubakar na PDP da ke bi a baya da kuri’u kusan miliyan bakwai, shi kuma Peter Obi da ya zo na uku ya samu kuri’u miliyan shida.

XS
SM
MD
LG