Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar SDP Tace Dan Takararta na Gwamna A Jihar Adamawa Na Nan Daram


Jam’iyyar SDP a Najeriya ta karyata rahotannin dake cewa ta janye dan takarar gwamnanta a jihar Adamawa, wannan kuma na zuwa ne a yayin da sabbin jam’iyyu ke tasowa a Najeriya.

A wajen wani taron manema labarai jam’iyyar SDP dake da alamar doki, shugabanin jam’iyar sun yi watsi da rahotannin da wasu ke yadawa na cewa zata janye dan takarar kujerar gwamnanta Chief Emmanuel Bello, inda ta danganta lamarin da yarfiyar siyasa, musamman a wannan lokacin da rikicin cikin gida ke dabaibaye wasu manyan jam’iyyu a Najeriya.

Jam’iyyar ta SDP dai ta ce ta shirya tsaf domin kwace goruba daga hannun kuturu. To wai ko me dan takarar gwamna na jam’iyar zai ce game da batun zai marawa wani dan takara baya a yanzu?

Chief Emmanuel Bello ya ce sharrini kawai saboda anga alamun zai ci zabe amma shi bai janye daga takara ba.

Kamar dai jam’iyyar SDP, ita ma wata sabuwar jam’iyya ta ANP, wato Alliance National Party tuni ta kammala fidda nata gwanayen don zaben dake tafe.

Alhaji Umar Bello Jada da akewa lakabi da Calculate, tsohon dan jam’iyyar PDP da APC ne, shi ya kawo sabuwar jam’iyyar ta ANP a Adamawa kuma shi aka tsayar a matsayin dan takarar gwamna, ya bayyana irin dammarar da suka yi.

To wai ko ya manyan jam’iyyu ke kallon tashin gwauron zabin da kananan jam’iyyu keyi a yanzu?

Sakataren tsare- tsare na jam’iyyar APC a jihar Adamawa Ahmed Lawal, ya ce bai yi tsammani akwai wata jam’iyya da zata kwatanta kanta da manyan jam’iyyun kasar ba a yanzu. Ya kara da cewa bai ga wata jam’iyya da zata taso yanzu da zata sami karbuwa wurin jama’a fiye da su ba.

Ga karin bayani cikin sauti.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG