Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyun Hamayya a Nijar Sun Mayar Da Martani Kan Jingine Zaben Mazauna Kasashen Waje


Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou

A jamhuriyar Nijer jam’iyun hamayya sun maida martani mako 1 bayan da kotun tsarin mulkin kasa ta bayyana cewa jingine zaben ‘yan kasar mazauna ketare saboda anobar covid 19 bai sabawa kundin tsarin mulki ba.

A cewarsu, matsayin kotun wata alama ce da ke nuni da cewa ita da hukumar zabe ta CENI dukansu 'yan amshin shata ne na jam’iya mai mulki ta PNDS TARAYYA saboda haka ba za su yi adalci a zaben da ake shirin gudanarwa a karshen shekarar 2020 ba, zargin da jam’iyar mai mulki tace shaci fadi ne.

A sanarwar da suka fitar, jam'iyun FRDDR da FOI da FP da FDR sun ce amsar da kotun tsarin mulkin kasa ta bayar a makon jiya bayan da fraim minista Birgi Rafini ya bukaci ta fayyace matsayin doka game da bukatar jingine zaben ‘yan Nijar mazauna kasashen waje, abu ne da "a fili ake gane an yi aiki da son rai."

A bisa la’akari da abinda suka kira kwan-gaba kwan-bayan da ake fuskanta akan maganar tsare tsaren zabe, shuwagabanin jam’iyun hamayya sun bukaci gwamnatin Niger ta rushe hukumar zaben kasar ko kuma mambobin hukumar su yi murabus.

Jam’iyar PNDS TARAYYA mai mulki wace ‘yan adawa ke dorawa alhakin abubuwan da ke faruwa a game da batun tsare tsaren zabubukan na karshen shekara ta yi watsi da dukkan wadanan zarge zarge.

A wani labarin na daban mai alaka da shirye shiryen zabe shugaba Issouhou Mahamadou ya sallami ministan cikin gida Bazoum Mohamed daga mukaminsa a cikin daren jiya, Litinin 29 ga watan Yuni da nufin ba shi damar tsara yakin neman zabe a matsayinsa na dan takarar jam’iyar PNDS TARAYYA a fafatawar ta watan December 2020.

Ga cikakken rahoton Souley Moumouni Barma.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG