Jami’ai a Nijar su na ci gaba da aikin rijista na kasa, na neman mutane su rika yin rijistar haihuwa, da mutuwa da kuma aure, a wani mataki na ba gwamnati damar bullo da manufofin raya kasa yadda ya kamata. Akasarin mutane a Nijar dai ba sa yin rijistar, abin da ya sa gwamnati shigo da sarakunan gargajiya domin ganin sun taimaka. Ga Yusuf Abdoulaye da rahoton daga Niamey.