Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jamhuriyar Nijer Za Ta Fara Zagaye Na 2 Na Kamfen Din Riga Kafin Covid 19


Allurar riga kafi.
Allurar riga kafi.

Yau talata 15 ga watan Yuni ake fara zagaye na 2 na kamfen riga kafin cutar covid 19 a jamhuriyar Nijer inda za a kafa asibitocin tafi da gidanka a mashigar ma’aikatun gwamnati tashoshin shiga motocin haya da filayen jirgin sama da gidajen hakimai da masu unguwa .

Lura da yadda annobar corona ke kara tsananta a wasu kasashen waje inda aka fara samin bular wani sabon nau’in kwayar cutar ya sa hukumomin Nijer soma yunkurin tsaurara matakan riga kafi mafarin wannan kamfe da za a fara a yau talata 15 ga watan yuni kamar yadda ministan kiwon lafiyar al’uma Dr Iliassou Idi Mainassara ya bayyana a taron manema labaran da ya kira.

Tuni aka kebe wasu wuraren musamman domin gudanar da wannan aiki na tsawon mako 1 saboda haka aka bukaci al’umma ta baiwa likitoci hadin kai.

Daga lokacin gano mutun na farko da ya kamu da cutar corona a nan Nijer a watan maris na 2020 kawo jiya litinin 14 ga watan Yuni mutum 5452 aka bayyana cewa sun harbu da kwayar cutar a wannan kasa daga cikinsu 5172 suka warke yayinda a yanzu haka mutum 88 ke asibiti domin karbar magani kuma bayanan hukumomin kiwon lafiya sunce mutane 192 ne cutar ta covid 19 ta kashe a tsawon wannan lokaci saboda ake kara kiran jama’a a ci gaba da biyayya ga matakan riga kafi.

Domin karfafa zagayen farko na allurar riga kafin da aka kaddamar a ranar 28 ga watan maris din da ya gabata ne hukumomin lafiya suka shirya zagaye na 2 da ke somawa daga yau talata 15 ga watan Yuni.

Saurari cikakken rahoton a cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00

XS
SM
MD
LG