Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an Amurka, China Da Rasha Na Kokarin Karfafa Dangantaka Da Afrika


US Africa Leaders Summit
US Africa Leaders Summit

Manyan jami'an kasashen China, Rasha, da kuma Amurka suna kokarin ziyartar kasashen Afirka a wannan watan don yin alkawarin ba da gudummuwa ga nahiyar da ke bunkasa cikin sauri a duniya.

Yayin da shugaba Joe Biden ke shirin kai ziyara nahiyar a cikin shekarar nan, manyan jami'ansa da yawa sun ziyarci Afirka a kwanan nan a kokarinsu na tabbatar da samun goyon bayan kasashen Afirka don dakile tasirin Rasha da kuma burin China, da daukar alkawarin yin aiki don alfanun Afirka.

Amurka ta ce matakin ziyarar ba wai don dakile tasirin Rasha da China ba ne kawai, duk da cewa Amurkar ta bayyana rashin jin dadinta game da yadda kasashen Afirka suka ki yin Allah wadai da mamayar da Rasha a Ukraine, amma don kulla dangantaka mai ma'ana a fannonin kasuwanci, kiwon lafiya, zaman lafiya, da tsaro.

"Hadin gwiwarmu a Afirka ba don sauran kasashe ba ne," a cewar Sakatariyar yada labaran fadar White House Karine Jean-Pierre a lokacin da take amsa tambayar da Muryar Amurka ta yi mata. Ta kuma ce hadin gwiwar Amurka a can, ta kasance kamar yadda alkawuranmu suka nuna a taron kolin shugabannin Amurka da Afirka. Amurka na kallon kasashen Afirka a matsayin abokan hulda na gaske kuma tana son kulla dangantaka bisa mutunta juna, a cewarta.

Amma babban jami'in diflomasiyyar nahiyar ya ce Afirka, wacce kasashen Turai suka yi wa mulkin mallaka tsawon shekaru masu yawa, ba wurin da wasu zasu yi amfani da shi ba ne don muradansu. Ya kara da cewa China ta fahimci hakan.

XS
SM
MD
LG