Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Amurka Za Su Bayyana a Gaban Majalisar Dokoki


Sakataren harkokin wajen Amurka, ranar 9 ga watan Mayu 2019.

A yau Talata, ake sa ran wasu manyan jami’an gwamnatin shugaba Trump, za su ba da bahasi a gaban Majalisar Dokokin Amurka, a wani zama da za su yi na sirri, kan batun barazanar da Fadar White House ta ce Iran na yi a Gabas ta Tsakiya.

Daga cikin jami’an, har da Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, mukaddashin Sakataren tsaron Amurka, Patrick Shanahan da kuma shugaban hafsan hafsoshin dakarun kasar, Janar Joseph Dunford.

Jami’an gwamnatin na Trump, za su gana ne da ‘yan majalisar, bayan zargin da suke cewa, Iran ce da alhakin kai wasu hare-hare akan wasu tashoshin man kasar Saudiyya da kuma wasu tankunan manta guda hudu.

Hukumomi Iran dai sun ce, su ba yaki suke so su yi da Amurka ba, amma dai ba su nuna sha’awar hawa taburin tattaunawa da Amurkan ba.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG