Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Diflomasiyar Kasashen Larabawa Sun Gudanar Da Ganawar Sirri Kan Makomar Gaza


Ministocin sun gudanar da taron share fagge da tuntubar juna da mayar da hankali a kan sake gina zirin da yaki ya daidaita ba tare da raba mazauna cikinsa su miliyan 2.4 da matsugunansu ba.

Ministocin harkokin wajen kasashen Larabawa sun yi ganawar sirri a birnin Alkahira a yau Litinin gabanin taron kolin kungiyar kasashen da ya mayar da hankali a kan kalubalantar shirin Shugaban Amurka Donald Trump na karbe iko da zirin Gaza tare da korar mazauna cikinsa.

Ministocin sun gudanar da taron share fagge da tuntubar juna da mayar da hankali a kan sake gina zirin da yaki ya daidaita ba tare da raba mazauna cikinsa su miliyan 2.4 da matsugunansu ba, kamar yadda wata majiya a kungiyar kasashen Larabawa ya shaidawa kamfanin dillancin labaran AFP, tare da neman a sakaya sunansa.

A cewar majiyar, an kange manema labarai daga halartar taron, inda yace za'a gabatarwa shugabannin Larabawa da shirin a taronsu na gobe Talata domin amincewarsa."

Gabanin taron, ministan harkokin wajen Masar Badr Abdellatty ya gudanar da wani taro na daban da takwarorinsa na kasashen Larabawa, ciki har da na Jordan, Bahrain, Tunisiya, Iraki, Yemen da kuma manyan jami'an diflomasiyar Falasdinu.

A yayin ganawar, Abdellatty ya bukaci a fara gudanar da ayyukan farfado da zirin Gaza ba tare da gusar da Falasdinawa daga yankinsu ba, kamar yadda sanarwar da ma'aikatar wajen Masar ta bayyana.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG