Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an DSS Sun Yi Dirar Mikiya A Gidan Surukin Tukur Mamu Sun Kuma Yi Awon Gaba Da Shi


Jami'an tsaro na DSS a Najeriya (Hoto: AP)
Jami'an tsaro na DSS a Najeriya (Hoto: AP)

Jami'an hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya ta DSS sun kai wani samame a gidan surikin mawallafin jaridar Desert Herald Mallam Tukur Mamu da tsakar daren ranar Alhamis inda suka yi awon gaba da shi zuwa ofishinsu.

Abdullahi Mashi, suriki ne ga Mamu, ya na tsare a ofishin jami'an DSS da ke birnin tarayya Abuja a halin yanzu, a cewar 'yan uwansa.

Dan uwan Tukur Mamu, Elfarouq Mamu, ya shaida wa Muryar Amurka cewa jami'an tsaron sun kuma kai irin wannan samamen gidan kanin matar Tukur mai suna Ibrahim Tinja, wanda yake tare da Tukur a kasar Masar lokacin da aka tiso keyarsu zuwa Najeriya.

Tun da farko dai gidan Mallam Tukur jami'an tsaron suka fara kai samame da kuma gidan wani babban jami'i a kamfanin jaridarsa ta Desert Herald mai suna Ibrahijm Mada a daren ranar Laraba, inda suka yi awon gaba da wasu muhimman takardu, wayoyin salula da kwamfutoci.

'Yan uwan Mamun sun ce jami'an na DSS sun sako matan Tukur su biyu, amma har yanzu suna ci gaba da tsare da shi da babban dansa Faisal Mamu, da kanen matarsa Ibrahim Tinja.

A baya dai Tukur Mamu shi ya yi ta shiga tsakanin gwamnati da 'yan ta'adda don ganin an sako fasinjojin jirgin kasan nan da 'yan ISWAP su ka yi garkuwa da su a watan Maris na 2022.

Amma daga bisani ya bayyanawa VOA cewa ya janye daga aikin shiga tsakanin bayan da ya yi koken ana yi wa rayuwarsa barazana.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG