Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaro Sun Garkame Kofar Shiga Fadar Shugaban Jamhuriyar Nijar


Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum
Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum

“Bayanai na nuni da cewa Shugaba Mohamed Bazoum na hannun dogarawan fadarsa." In ji wakilin Muryar Amurka a Yamai, Souley Moumouni Barma.

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa, jami'an tsaro sun rufe duka hanyoyin shiga fadar shugaban kasar, a wani lamari da ba a fayyace takamaiman abin da ke faruwa ba.

Wakilin muryar Amurk a Yamai Souley Moumouni Barma ya ce da safiyar Larabar nan an hana duka ma'aikata shiga fadar shugaban kasar.
“Bayanai na nuna cewa Shugaba Mohamad Bazoum na hannun dogarawan fadarsa.

“Kawo yanzu ba a ji karar bindiga ko guda daya ba, yayin da jama’a ke ci gaba da gudanar da harkokinsu a kewayen fadar shugaban kasar.” In Souley Moumouni Barma.

Harkoki na ci gaba da gudana a sauran yankunan birnin na Yamai yayin da motoci ke ci gaba da zirga-zirga kamar yadda suka saba a cewar kamfanin Dillancin Labarai na Reueters.

Lokaci na karshe da aka yi yunkrin juyin mulki a kasar ta Nijar mai makwabtaka da Najeriya shi ne a watan Maris din 2021, kwanaki biyu gabanin shugaba Mohamad Bazoum ya karbi mulki.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG