Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an Tsaro Sun Ceto Mutum 58 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Jihar Kogi


'Yan sandan kwantar da tarzoma a Najeriya
'Yan sandan kwantar da tarzoma a Najeriya

Jami’an tsaron Najeriya sun ceto mutane 58 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a tsakiyar jihar Kogi, kusa da babban birnin tarayya Abuja.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce an kashe daya daga cikin wadanda aka sace yayin aikin ceto kuma masu garkuwa da mutanen sun tsere.

Hukumomin ‘yan sanda a cikin wata sanarwa da suka fitar ranar Lahadi, sun ce aikin ceton wani bangare ne na ayyukan da jami’an tsaro ke yi na yaki da munanan laifuka, ta hanyar ceto wadanda aka kashe da kuma kama masu laifi a kewayen Abuja, babban birnin tarayya da kuma jihohi makwabta.

An dai yi garkuwa da mutanen ne a wani daji da ke gundumar Gegu a jihar ta Kogi.

‘Yan sanda sun ce masu garkuwa da mutane sun yi artabu sosai a lokacin da jami’an tsaro suka isa wurin, amma sun ce jami’an tsaro sun yi galaba a kansu tare da raunata da dama daga cikinsu kafin su gudu, inda suka bar wadanda abin ya shafa.

Kwamishinan ‘yan sandan Abuja Haruna Garba ya shaidawa Muryar Amurka ta wayar tarho cewa, an ceto mutane 58 da aka yi garkuwa da su a harin na Gegu da sauran su.

‘Yan sanda sun ce daya daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su da suka samu raunuka yayin aikin ceto Gegu ya mutu nan take. Sun ce sauran wadanda aka ceto za a sake hadasu da iyalansu bayan an duba lafiyarsu.

Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro da dama amma garkuwa da mutane na daga cikin kalubalen da suka fi daukar hankali.

Abuja ta samu kwanciyar hankali duk da jihohin da ba su da nisa da ita suna fama da tashe-tashen hankula da suka hada da yawaitar hare-haren garkuwa da mutane domin neman kudin fansa.

Wani mai sharhi kan harkokin tsaro, Sanata Iroegbu, ya ce rashin tsaron da ake fuskanta ba zai rasa nasaba ba da fasa gidan yari da aka yi a Abuja a shekarar da ta gabata, wanda aka yi nasarar kubutar da daruruwan masu aikata laifuka ciki har da wadanda ake zargi da ta'addanci.

A ranar 29 ga watan Mayu ne za a rantsar da zababben shugaban Najeriya, Bola Tinubu, inda aka rika sukar wanda ya gabace shi da rashin samar da isasshen tsaro a kasar.

XS
SM
MD
LG