Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami’an Tsaron Gwamnatin Tarayya Za Su Fara Ficewa Daga Birnin Portland


Gwamnan jihar Oregon da ke arewa maso yammacin Amurka, Kate Brown ta ce, a yau Alhamis jami’an tsaro na gwamnatin tarayya za su fara ficewa daga birnin Portland, bayan wata matsaya da suka cimma tsakaninsu da jami’an gwamnatin tarayya.

Ita dai gwamnatin ta tarayya ta kare matakin da ta dauka na tura jami’an tsaron, tana mai cewa ta yi hakan ne domin a maido da doka da oda da suka subucewa hukumomin jihar, na zanga-zanga da da ta ki ci ta ki cinyewa, lamarin da ta ce yana saka gine-gine gwamnatin tarayyar cikin hadari

Ita dai gwamna Brown ta kasance daya daga cikin wadanda suke sukar matakin tura jami’an tsaron, inda a jiya Laraba ta zarge su da “yin mamaya da kuma haifar da tarzoma,” tana mai cewa lamarin ya sa ana ta barnata dukiyoyi a tsakiyar birnin na Portland.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG