Jami’an tsaron kasar Sri Lanka, sun yi wani artabu da wasu ‘yan bindiga a yankin da ake kira Kalmunai a gabashin kasar.
Wani kakakin sojin kasar, ya ce an samu gawarwakin mutum 15, shida daga cikinsu na kananan yara ne a gidan da aka yi musayar wuta tsakanin jami’an tsaron da ‘yan bindigar.
Jaridar Daily Mirrow da ake bugawa a kasar ta Sri Lanka, ta wallafa cewa, an ji wata fashewa a lokacin da jami’an tsaro suka yi yunkurin cajin wani mutum.
Dakarun sun ce sun samu sinkin ababan fashewa, da uniform din mayakan kungiyar IS, da karamin jirgi mai sarrafa kansa, da kuma na’ura mai kwakwalwa kirar tafi-da-gidanka.
Facebook Forum