Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaron Afghanistan 100 Ne Suka Mutu A Yakin Ghazni


Jami'an tsaron Afghanistan suna sintiri cikin birnin Ghazni

Jiya Litinin mahukumtan Afghanistan suka tabbatar cewa dakarun kasar 100 ne suka rasa rayukansu kana fararen hula kimanin 30 su ma suka sheka lahira a yakin da suke gwanzawa a garin Ghazni

Mahukuntar kasar Afghanistan sun tabbatar jiya littini cewa fadan da aka kwashe kwanaki 4 ana gwabzawa da ‘yan tawayen Taliban a ciki da wajen garin Ghazni dake kudu maso gabashin kasar yayi dalilin mutuwar jamia’an tsaron kasar har su 100 da kuma wasu farar hula su 30.

Minisatan tsaron kasar Janar Tariq Shah Bahrami yace sojojin gwamnati dake da goyon bayan sojojin taron dangi dake yaki ta sama sunyi nasarar kashe sojojin sa kai har kusan 200 ciki ko harda da Larabawa,da ‘yan Checheniya, dama ‘yan Pakistan.

Bahrami ya lashi takobin ganin an kawo karshen wannan al’amari a cikin babban birnin kasar nan da ‘yan kwanaki, domin za a kakkabe duka ‘yan Taliban cikin babban birnin kasar.

Sai dai mai Magana da yawun Taliban din Zabuhullah Mujahidin nan take yayi watsi da wannan sanarwan ta minstan tsaro yana cewa ai sojojin sa kai sun riga sun kewaye sojojin Afghanistan a wasu sassan babban birnin kasar.

Sai dai kawo yanzu ba a tantance gaskiyar wannan sanarwan ta ‘yan tawaye daga wata kafa ta fisabilillahi ba, domin sau tari suna kara gishiri game da nasarar da suka samu a lokacin yaki

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG