Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Amurka Da Na China Sun Fara Tattaunawa Kan Harkokin Cinikayya


A cikin makonnin nan, muhawara ta kara zafafawa biyo bayan barazanar da Trump yayi na sanyawa kayayyakin China tarar dala biliyan 50 domin ladabtar da Beijing kan abin da gwamnati ta kira rashin adalcin a tsare tsarenta na harkokin cinikayya.

Wadansu manyan wakilan harkokin cinikayya na Amurka sun fara tattaunawa da jami'ian kasar China a Beijing, yayinda Washington take kokarin shawo kan damuwar da ake da ita dangane da tsare tsaren tattalin arzikin kasar China. Wadansu na ganin taron a matsayin wani matakin da ka iya haifar da abu mai kyau, yayinda bangarorin biyu ke kokarin kaucewa barkewar rashin jituwa a harkokin cinikayya.

Masu sharhi kan lamura sun ce ba lallai ne su warware bambance bambancen dake tsakanin su a wannan zaman tattaunawar ba, amma za a yi na'am da shawarar, da ci gaba da ganawa.Shugaban Amurka Donald Trump a shafinsa na Twitter ya ce jami'ai na kokarin tattaunawa akan samun daidaito a bangaren kasuwanci.

Raymond Yeung, babban ma'aikaci a fanin tattalin arziki wa China a bankin Australiya da New Zealand, ya ce idan bangarorin biyu za su yarda su cigaba da tattaunawa zai zama babban cigaba. Bambance bambance kan tsare tsaren harkokin cinikayya da samun shiga kasuwani sun kasance batutuwa da suka tsonewa Amurka ido da wasu masu saka hanu jari daga kasar waje a China.

Beijing dai ta musanta zargin da Washington ke yi kuma ta dage cewa tana kara bude kasuwaninta. kwanan ta yi alkawarin zata cire tarar kashi 25 kan motacin da ake shigowa da su daga kasashen waje, albeit a shekarar 2022.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG