Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Koriya ta Arewa da ta Kudu Sun Gana Domin Karfafa Zumunci


Janar An Ik San na Koriya ta Aewa da Manjo Janar Kim Do-gyun sun sha hannu a taronsu a kauyen Panmunjon
Janar An Ik San na Koriya ta Aewa da Manjo Janar Kim Do-gyun sun sha hannu a taronsu a kauyen Panmunjon

A wani yunkurin karfafa zumunci jami'an Koriya ta Arewa da ta Kudu sun gana a wani kayuen Panmunjon domin tattaunawa jiya Talata

Jami’an sojin Korea ta Arewa da makwabciyarta ta Kudu, sun gana a jiya Talata a kauyen Panmunjom, a wani sabon yunkuri na kara dakon zumunci yayin da kasashen biyu ke karfafa dangantakarsu a wani mataki na tsallaka kan iyakokinsu.

Koriyoyin biyu dai sun amince su tattauna kan batun rage yawan dakaru da makamai a yankin nan da babu soji ko makamai.

Tattaunawar ta kasance ne, a yayin da wani babban jami’in Amurka ya ce hotunan tauraron dan adam, sun gano wasu sabbin ayyuka da ake yi a tashar Sanumdong da ta samar da makamai masu linzami na farko da kasar ta mallaka, duk da cewa Amurka na ganawa da hukumomin Pyonyang, kan yadda za su wargaza makaman na nukiliya.

A ranar Litinin, Jaridar Washington Post ta ruwaito wasu jami’ai da a ba a bayyana sunayensu ba, suna cewa akwai alamu Korea ta Arewan na sake gina sabbin makamai masu linzami wadanda ke amfani da mai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG