Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Koriya Ta Arewa Ba Ta Dakatar Da Kera Makaman Nukiliya Ba


Makami mai linzamin da Koriya Ta arewa ta nuna a wani faretin soja da aka gudanar a watan Fabrairu.

Jaridar Washington Post ta ruwaito cewa hukumomin leken asirin Amurka sun ce bisa dukkan alamu Korea ta Arewa na kera wasu sabbin makamai masu linzami.

Jaridar tace ta bakin wasu jami’ai da basu yarda a ambaci sunayen su ba, sun ce akwai yiyuwar Korea ta Arewa tana kera akalla makami mai linzami guda watakila kuma biyu a wani wurin binciken ta dake Sanumdong.

Jaridar ta ce wani sabon shaidar yin hakan ko ya hada da hotunan da tauraruwar dan adam ta dauka, wanda ya nuna cewa makamin mai irin wanda yake amfani da mai ne, kuma yana iya kai wa Amurka.

Ko a cikin makon da ya gabata sai da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya ce har yanzu Korea ta Arewa tana samar da man da ake anfani da shi wajen sarrafa makaman kare dangi, duk alkawari da ta yi cewa za ta wargaza makaman nukiliya da ta ke da shi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG