Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu 'Yan Majalisar Amurka Sun Fadi Dalilan Korar Shugaban FBI


Tsohon Daraktan Hukumar Binciken Manyan Laifuka James B. Comey

Tun shekaran jiya da aka kori shugaban hukumar binciken manyan laifuffuka ta FBI waeo James Comey, ake ta cece-ku-ce a nan Amurka musamman tsakanin 'yan siyasa. Ko a yau ma sai da Majalisar kasa ta saurari jin ba'asin lamarin na korar jami'in.

Wasu jami’an majalisar dokokin Amurka sun ce shugaban hukumar binciken sirri ta FBI, James Comey da aka kora ya nemi karin kudade da kayan aiki. Domin ci gaba da binciken da ya ke yi game da katsalandan da ake zargin Rasha ta yi a lokacin zaben shugaban kasa a shekarar da ta gabata da kuma yiwuwar ko akwai wata alaka tsakanin Rasha da ýan kwamitin yakin neman zaben shugaba Donald Trump.

Jami’an sun ce Comey ya gabatar da bukatar ne ga mataimakin shugaban ma’aikatar shari’ar kasar Rod Rosenstein, wanda tare da shi kansa shugaban ma’aikatar Shari’ar, Jeff Sessions suka bayyana hujjojin da suka sa gwamnatin Trump ta kori Comey.

Sai dai ma’aikatar shari’a ta musanta cewa an gabatar mata da wannan bukatar. Ba a dai san ko dalilin wannan bukatar ne ya sa Trump yanke shawarar korar Comey ba. Masu sukar lamiri akan korar da aka yiwa shugaban hukumar ta FBI sun ce akwai ayar tambaya akan binciken da hukumar ke yi.

Korar Comey da aka yi ta janyo kiraye kiraye musamman ma daga ‘yan majalisa, ‘yan jam’iyyar Democrat akan bukatar samo wani lauya mai zaman kansa na musamman don ya binciki yiwuwar katsalandan Rasha. Amma kakakin majalisa Paul Ryan da wasu shugabannin jam’iyyar Republican sun yi watsi da wannan kiran.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG