Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaro Sun Afka Wa Masu Zanga Zanaga A Kasar Habasha


Mummunar zanga-zangar da ta auku a kasar Habasha cikin satin da ya gabata ta biyo bayan yawan takurawar da wani bangaren kasar yake ganin ana yi masa ne.

Sai dai kuma wannan zanga-zangar na iya kawo manya-manyan kabilun kasar waje daya domin kuwa sun ce abu guda ke damun su.

Wannan ne yasa wasu masu kula da al’amurran yau da kullun ke cewa ba mamaki a sake samun wani sabon tashin hankali a kasar

Yanzu haka dai kusan mutane 100 aka kashe kuma jami’an tsaro ne suka auka masu suka murkushe wadannan masu zanga-zangar a cikin karshen satin daya gabata.

Jamiyyar adawa ta kasar ita da kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesaty International suka ce jami’an tsaro sun bude wa masu zanga-zanga wuta, abinda yayi dalilin mutuwar wasu daga cikin su.

Gwamnatin kasar ta Habasha tace wannan ba laifin kowa bane illa na ‘yan adawa domin ko sune suka shirya zanga-zanga bada neman izinin yin hakan ba.

Mai Magana da yawun gwamnatin kasar yace masu zanga-zangar wasu daga cikin su na dauke da makamai ciki ko harda bamb.

Sai dai ‘yan adawa sunce wannan zuki ta mallaki ce masu zanga-zangar basu dauke da kowane irin makami kuma suna gudanar da zanga-zangar su cikin lumana.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG