Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru da Kasashen Turai Sunyi Yarjejeniyar Kawar da Haraji Kan Kayan da Suke Sayarwa Junansu


Shugaban kasar Kamaru Paul Biya
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya

Shugaban kasar Kamaru ya rabtaba hannu kan wasu yarjeniyoyi da kasar tayi da kasashen nahiyar turai kan shigo da wasu kaya cikin kasar ba tare da biyan haraji ba.

Haka ma ita kasar Kamaru din zata dinga aika da kayanta domin sayarwa ba tare da biyan haraji ba.

Jakadiyar kasashen nahiyar Turai Francois Collett ta yaba da yarjejeniyar da kasar Kamaru ta cimma da kasashen Turai. Tace lamarin zai taimakawa kasar ta Kamaru musamman wajen farfado da tattalin arzikin kasar.

Alhaji Tanimu Bafan wanda ya kasance babban dan kasuwa yace yarjejeniyar zata kawowa harkokin kasuwanci cigaba. Kawar da haraji ma kayan kasar a Turai zai taimaka. Yace kamar ayabar Kamaru idan sun kaita Turai suna biyan haraji. Ta bangaren talakawa, magunguna da ake shigowa dasu daga Turai zasu yi araha, lamarin da zai rage masu radadin talauci.

Ga rahoton Awal Garba da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:36 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG