Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an tsaro suna sintiri a kan titunan babban birnin kasar Tunisiya, kwana daya bayan tserewar dadadden shugaban kasar


Masu zanga zanga a kan tituna.

Jami'an tsaro suna sintiri a kan titunan babban birnin kasar Tunisiya, kwana daya bayan tserewar dadadden shugaban kasar

Yan sanda da tankokin rundunar soji suna sintiri a babban birnin kasar Tunisiya yau asabar, kwana daya bayan da wata kazamar zanga zanga ta tilastawa shugaban kasar barin mukamin. Daruruwan sojoji ke sintiri bisa titunan Tunis da ke cike da jibgin shara bayan an kwana zanga zanga da kwasar ganima a shaguna. Shugaba Zine El Abidine Ben Ali, ya tsare daga kasar zuwa Saudaiya jiya jumma’a bayan shafe makonni ana zanga zanga bisa tituna sakamakon rashin ayyukan yi da kuma albazarancin jami’an gwamnati. A kalla mutane ishirin da uku ne aka kashe a tashin hankalin. Majalisar tsarin mulkin kasar ta yanke hukumci yau asabar cewa, mulkin Mr. Ben Ali ya kare, ta kuma ce kakakin majalisa Foued Mebezza zai karbi iko a matsayin shugaba na wucin gadi. Ta kuma bashi watanni biyu ya gudanar da zaben shugaban kasa. PM Mohammed Ghannouchi ya sanar da farko cewa, zai karbi iko a matsayin shugaban kasa na wucin gadi kafin tabbatar da cewa, Mr. Ben Ali ba zai sake dawowa bisa kujerar shugabanci ba.

XS
SM
MD
LG