Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya Na Shirin Zuba Sojoji Dubu 11 A Mali


Jami'an Majalisar Dinkin Duniya suna ganawa akan Mali.

Ana kyautata zaton Majalisar dinkin duniya zata amince da wani kuduri yau alhamis na girka dakarun zaman lafiya a Mali.

Kasar Mali din ta shiga tashin hankali a shekarar da ta wuce, bayan da sojoji sun hambare gwamnati, kuma mayakan buzaye da kuma al-qaida daga baya suka kame arewacin kasar. Sojojin Faransa da Afirka sun taimaka wajen korar masu kishin Islaman daga manyan garuruwa, amma har yanzu dai hare-hare na cigaba.

Kudurin yayi kiran da a samar da sojoji dubu 11 da 200 da ‘yan sanda 1,400 da zasu share shekara daya a wannan waje. Zasu karbi aikin tsaron wajen ran 1 ga watan Yuli daga hannayen sojojin Afirka su dubu 6. Wasu daga cikin sojojin Afrikan zasu shiga cikin dakarun zaman lafiya na MDD da zasu zauna a can Mali din.

Idan kwamitin tsaron ya amince da wannan kuduri, to fa yana da kwana 60 ya tantance idan ‘yan ta’adda na da muguwar barazana ga Mali. Kwamitin na da damar dakatar da zuba sojojin idan abubuwa a Mali suka yi tsamari.
XS
SM
MD
LG