Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaron Jamhuriyar Congo Sun Bude Wuta Kan 'Yan Adawa


Shugaban Jamhuriyar Congo, Denis Sassou-Nguesso wanda yake son ya canza kundun tsarin mulkin kasar domin ya yi tazarce
Shugaban Jamhuriyar Congo, Denis Sassou-Nguesso wanda yake son ya canza kundun tsarin mulkin kasar domin ya yi tazarce

A jiya Talata jami’an tsaro sun bude wuta a jamhuriyar Congo, a lokacin suka yi arangama da masu zanga-zangar rashin amincewa da yunkurin shugaban kasar Denis Sassou N’guesso na kara wa’adin mulki.

Kamfanin dillancin labarun Faransa ya ruwaito cewa, an kwantar da akalla mutane 6 a asibiti sakamakon harbin bindiga bayan taho mu gamar a Brazzaville babban birnin kasar.

A ranar Lahadi mai zuwa ne kasar zata kada kuri’ar kan kwaskwarimar sabon kudurin kundin tsarin mulkin kasar, wadda za ta rushe wa’adin mulki 2 na shugaban kasa da kuma kayyade shekarun dan takarar shugabancin kasa ba zasu haura saba’in ba.

Kakakin ‘yan adawa da yunkurin kwaskwarimar Tsomambet Anaclet, ya fadawa sashen Faransanci na Muryar Amurka cewa, karon arangamar ranar Talatar ya fara ne a lokacin da ‘yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zangar da suke kokarin taruwa.

Shedun gani da ido sun ce, ‘yan sandan sun buga barkonon tsohuwa tare da bude wuta da bindiga. Haka zalika rahotanni sun bayyana cewa a ranar hanyoyin sadarwar ta internet ba sa aiki a mafi yawancin sassan birnin.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG