Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yinkurin Kwaskware Kundin Tsarin Mulki a Janhuriyar Dimoradiyyar Congo Na Janyo Rigima


Shugaban Congo Denis Sassou-Nguesso
Shugaban Congo Denis Sassou-Nguesso

Mutanen Janhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun tashi haikan wajen yin fito-na-fito da yinkurin canja kundin tsarin mulkin kasar, wata al'ada ta 'yan siyasar Afirka masu neman yin tazarce

A yau Talata, ‘Yan sanda a Jamhuriyar Congo sun yi amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga zangar adawa da yukurin yiwa kundin tsarin mulkin kasar gyaran fuska, abin da suka ce mataki ne na baiwa shugaba Denis Sassou N’guesso damar ci gaba da zama a kan karagar mulki.

Rahotanni sun ce masu zanga zangar sun kona tayun motoci tare da saka shingaye akan titunan Brazzaville, babban birnin kasar, yayin da aka katse hanyoyin sadarwa na wayar talho da kuma yanar gizo ko kuma intanet.

A ranar Lahadi mai zuwa, za a gudanar da kuri?ar raba gardama kan ko ya dace a yiwa kundijn tsarin mulkin garanbawul ko kuma a?a.

Idan har aka amince da yin sauyin ga kundin tsarin mulkin, hakan zai kawar da tsarin yin wa’adin biyu ga shugabannin kasar da kuma shekaru 70 da ba a so su wuce.

Idan har aka gaza yin sauyi ga kundin tsarin mulki, hakan zai hana shugaba Sassou Nguesso damar ci gaba da mulkar kasar, wacce ya kwashe sama da shekaru 30 ya na gudanar da harkokinta.

XS
SM
MD
LG