Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Zaben Jihar Michigan Sun Tabbatar Trump Ne Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa


Donald Trump, shugaban Amurka mai jiran gado
Donald Trump, shugaban Amurka mai jiran gado

Jami’an Hukumar zaben jihar Michigan dake nan Amurka sun tabattarda cewa Donald Trump ne ya lashe zaben shugaban kasa da aka yi, inda ya zarce Hilary Clinton da kuri’u kalilan da basu shige 10,704 daga cikin kusan kuri’u milyan hudu da aka jefa a lokacin zaben ba.

Sanarwar da jamii’an suka bada jiya Litinin ta tabattar ke nan cewa Trump ne kuma ya kwashe dukkan kuri’u 16 na jihar na mazabun jiha.

Sai dai kuma duk da haka har yanzu akwai yiyuwar cewa karshenta sai an sake kira kuri’un da aka jefa a wannan jihar ta Michigan da kuma wasu jihohi biyu na Wisconsin da Pennsylvania in da ratar dake tsakanin ‘yan takaran bata da yawa kwarai.

Tuni wata ‘yar takarar shugaban kasa ta jam’iyyar Green Party da ake kiran ta Jill Stein ta shigar da takardun bukatar neman a sake kirga dukkan kuri’un da aka jefa a Pennsylvania da Wisconsin, kuma tace nan gaba kadan zata nemi ita ma jihar Michigan, a sake kirga nata kuri’un.

Idan aka sake kirga kuri’un kuma aka juye zaben a wadanan jihohin, to dukkan kuri’u 46 na mazabuna jihohin guda ukku za’a bada su ne ga Hilary Clinton, abinda zai sa a tumbuke Donald Trump daga wanda ya lashe zaben.

Sai dai masana tsarin siyasar Amurka sunce da kyar hakan ta faru.

XS
SM
MD
LG