Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyar Muslim Brotherhood tana neman goyon bayan sauran jam'iyu


Ana harhada sakamakon zabe a kasar Misira

Jam’iyar Muslim Brotherhood ta gayyaci ‘yan takarar shugaban kasar da suka sha kaye zuwa wani taro da za a gudanar gobe lahadi

Jam’iyar Muslim Brotherhood ta gayyaci ‘yan takarar shugaban kasar da suka sha kaye zuwa wani taro da za a gudanar gobe lahadi a yunkurin neman marawa dantakararta Mohammed Morsi baya, wanda bisa ga dukan alamu zai je zagaye na biyu da dan takarar jam’iyar da bata hada harkokin addini da siyasa Ahmed Sharif.

Kakakin kungiyar kishin islaman ya yi kira ga sauran ‘yan takarar goma su ceci abinda ya bayyana a matsayin “juyin juya hali” yayinda yake basu goron gayyatar jiya jumma’a.

Sakamakon zaben da ba a hukumance aka bayar ba, na zaben da aka gudanar ranar Laraba da kuma alhamis na nuni a cewa, Morsi yana kan gaba yayinda Shariq yake biye kurkusa.

Shariq shine firai minista a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Hosni Mubarak da aka hambare.

Za a sanar da cikakken sakamakon zaben ranar Talata. Yayinda za a gudanar da zaben fidda gwani ranar sha shida da sha bakwai ga watan Yuni

Dubi ra’ayoyi (1)

An rufe wannan dandalin

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG