Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyar PDP na Gaba a Sakamakon Jihohi 8 da Abuja


Shugaban Hukumar Zabe ta INEC Farfasa Attahiru Jega a Abuja, Maris 30, 2015.

An fara bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar da Lahadi.

A halin yanzu sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar Asabar da Lahadi a Najeriya, ya fara fitowa. Zuwa yanzu an bayyanar da sakamakon jihohi 8 da birnin tarayyar Abuja. Bisa ga wadannan sakamako da aka fitar a wadannan jihohin jam’iya mai mulki ta PDP ita ke da rinjaye da kuri’u 2,322,734, ita kuwa jam’iyar adawa ta APC na biye da kuri’u 2,303,978 .

Amma nan da wasu sa’o’I kadan za’a cigaba da bayyanar da kuri’un a cewar shugaban hukumar zaben Farfesa, Attahiru Jega. A na kuma sa ran a bayyanar da kimani sakamakon jihohi 10 a nan gaba. Wanda sauran sakamakon sai zuwa gobe a cewar Jega.

XS
SM
MD
LG