Jam'iyyar ACN cikin takardar sanarwa d a ta aikewa kafofin yada labarai ciki har da Muriyar Amurka tace shugaban kasan ya maida mulkin Najeriya tamkar wasan yara. Kamara yadda zaku jin karin baya ni cikin wannan rahoto da wakilinmu na Ikko, Ladan Ibrahim Ayawa ya aiko mana.
Jam'iyyar ACN Tana Kira Ga Wakilai A Tarayya Su Tsige Shugaba Jonathan
Sakamakon irin matsaloli da suka kunno kai a wasu sassan Najeriya da kuma sabo yanzu a jihar Rivers, jam'iyyar hamayya ta ACN tana kira da a tsige shugaba Jonatahan sabo da rashin iya mulki.