Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Adawa Na Kan Hanyar Samun Gagarumar Nasara a Zaben Myanmar


Shugabar jam'iyyar NLD Aung San Suu Kyi tana yiwa magoya bayanta jawabi
Shugabar jam'iyyar NLD Aung San Suu Kyi tana yiwa magoya bayanta jawabi

Bayan an kwashi tsawon shekaru 25 babu harkokin siyasa ko zabe, jam'iyyar adawa ta Aung Suu Kyi ta kama hanyar lashe zaben da aka y jiya a kasar ta Myanmar a karkashin gwamnatin soja.

Jam'iyyar 'yar adawar Myanmar Aung San Suu Kyi ta samu kujerun fark a zaben da ake kyautata zaton zata samu gagarumar nasara. An yi zaben 'yan majalisu ne ranar Lahadi.

Jami,an zabe sun fada jiya Litinin cewa jam'iyyar National League for Democracy ta lashe kujeru 12 a birnin Yangon.

Sakamakon farko na wannan zaben an bayyana ne jim kadan bayan da Aung Suu Kyi ta bayyana karfin gwuiwar da take dashi cewa jam'iyyarta zata lashe zaben mai dimbin tarihi a cikin jawabin da ta yiwa magoya bayan jam'iyyar a hedkwatarta dake Yangon.

Amma bata yi ikirarin ta lashe zaben duka ba saboda har yanzu ana cigaba da kidaya.

Ta gargadi magoya bayanta kada su kuskura su takali 'yan takarar da suka fai zabe.

Kakakin jam'iyyar Win Htein ya gayawa manema labarai cewa jam'iyyarsu ta lashe kashi 70 na kuri'un da aka kada a duka fadin kasar. Sun yi wannan kiyasin ne bisa ga bayanan da aka tara ta hanyar da bata gwamnati ba.

XS
SM
MD
LG