Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Adawa PDM, Ta Nada Sabon Shugaba


Munir Garba Waziri, sabon shugaban jamiyyar adawa PDM

Kaddamar da Munir Garba Waziri a matsayin shugaban jam'iyyar adawa PDP da kwamitin zartaswanta yayi ya kawo karshen shugabancin Bashir Ibrahim Yusuf

Jam'iyyar PDM ta zargi tsohon shugabanta Bashir Ibrahim Yusuf da barin jam'iyyar kara zube da kuma neman hade jam'iyyar da wasu jam'iyyun siyasa biyar.

Shugabannin jam'iyyar sun yi dafifi a Abuja domin daukan matakin nada sabon shugaba lamarin da wasu suke ganin hakan tamkar fara kemfen din tsayar da dan takara ne a zaben 2019 da zai kara da jam'iyyar APC mai mulki yanzu.

Taron shugabannin jam'iyyar PDM a Abuja
Taron shugabannin jam'iyyar PDM a Abuja

Jam'iyyar bata musanta alaka da tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ba amma tace kawo yanzu ba dan jam'iyyar ba ne. Tace zata yi maraba dashi idan ya shigo jam'iyyar.

Aminu Gwandu wani dan kwamitin zartaswar jam'iyyar yace babu abun mamaki idan Atiku ya shigosu yace zai yi takarar shugaban kasa. Yace jagoranci ne kuma rashin jagorancin ya sa aka tube Goodluck Jonathan. Injishi shi ma Buharin idan bai gyara abubuwan da ake zarginshi a kai ba to zai gane kuskurensa a zaben shekarar 2019.

Sabon shugaban rikon kwarya yayi alkawarin farfado da jam'iyyar. Yace kofarsu a bude take su saurari shawarwari daga 'yan jam'iyyar.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

XS
SM
MD
LG