Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam’iyyar Adawa Ta Cambodia Ta Taka Rawar Gani


Masu kada kuri'a a zaben Cambodia

Babbar jami’iyar adawa a Cambodia ta taka rawar gani a zaben kananan hulumomi a jiya Lahadi wanda ke yin barazana ga Firayi Minista Hun Sen dake rike da mulki.

Da yake sanar da sakamakon zaben majalisar dokoki, kakakin jami’iyar adawar Yim Sovann, ya ce jami’iyarsa ta lashe kashi 46 cikin dari na yankunan, wanda ya yi sama da kashi 30 cikin dari da ta samu a zaben kananan hukumomi shekaru biyar da suka gabata.

Sovann ya fada a wani taron manema labarai cewar wannan wata gagarumar nasara ce ga jami’iyarsa ta Cambodia National Rescue Party.


Wani dandalin labaran gwamnati yace sakamakon da suka fara fitowa na nuna jami’iyar adawar ta lashe kashi daya cikin uku na yankunan.

A ranar 25 ga wannan watan Yuni ne za a bada baki dayan sakamakon zaben a hukumance.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG