Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ISIS Ta Dauki Alhakin Harin London


Kungiyar ISIS ta dauki alhakin kai mummunar harin da ya yi sanadiyyar asarar rayuka da yammacin shekaranjiya Asabar a birnin London, inda mutane bakwai suka mutu wasu 48 kuma suka jikata.

ISIS ta bayyana ‘dauki alhakin kai wannan hari da jami’anta na London suka kai a shafin labaranta na yanar gizo na Amaaq.

Direban babbar wata mota ya abkawa masu tafiya a ‘kasa a babbar gadar London. Mutane uku da suka sauko daga cikin motar suka sukar mutanen dake cin kasuwanci a wurin.


Sakataren harkokin cikin na Birtaniya Amber Rudd ya fada a jiya Lahadi cewar yan sanda sun kyautata zaton mutane uku da suka harbe su kadai ne suka kai wannan harin.


Amma dai yan sandan sun gaggauta bazuwa suna farauta ko kila za a samu wasu masu hannu a wannan harin. Tuni dai an kama mutane 12 tun daga daren Asabar din.


Ya zuwa yanzu gwamnatin Birtaniya bata shirya dage matsayin barazanan ta’addanci a cikin kasar daga matsakaici zuwa mai tsanani ba.

Facebook Forum

Wata manhaja mai saukaka wahalar samun gidan abinci na halal ga Musulman dake zaune a kasashen Turai
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG